Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da juyin mulkin a kasar Burkina Faso.
Wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun babban sakataren ta ce, mista Ban ya ba da umarnin da gaggauta sakin manyan jami'an gwamnatin kasar da ake tsare da su, kuma wajibi ne a koma kan tsarin shirye shiryen mika mulki a kasar, wanda ya yi daidai da dokokin kundin tsarin mulkin kasar, da kuma dokar mika mulki ta kasar.
Kazalika Ban Ki-moon ya nuna damuwarsa kan batun tabarbarewar tsaro a kasar, inda ya bukaci sojoji da jami'an tsaron kasar da su bi duk hanyoyin da suka dace don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, sannan su tabbatar da mutunta hakkin al'ummar kasar. (Ahmad Fagam)