in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An damke mutane 56 da ake zaton mayakan Boko Haram ne a yankin tsakiyar Najeriya
2015-09-23 09:37:21 cri

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa, ta kama mutane 56 a yankin tsakiyar kasar wadanda ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kogi Emmanuel Ojukwu ya shaidawa manema labarai a Lokoja, fadar mulkin jihar cewa, an damke wadanda ake zargin ne a maboyarsu daban-daban da ke kauyen Obajana da ke wajen birnin Lokoja.

Ojukwu ya ce, 'yan sandan sun kaddamar da samamen ne, sakamakon wani hari da aka kaiwa motar sintirin 'yan sandan a kauyen Obanaja a ranar 14 ga watan Satumba wanda ya yi sanadiyar halaka wani sipeton 'yan sanda.

Kwamishinan ya ce, 'yan sandan sun yi nasarar kwato muggan makamai da kwayoyin sa maye a yayin wannan samame, kuma nan ba da dadewa ba za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China