in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun cafke wadanda ke samarwa Boko Haram abinci
2015-09-17 10:19:22 cri

Rundanar sojan Najeriya ta fada a ranar Larabar nan cewar, ta samu nasarar damke mutane 33 da take zargin su ne ke samarwa kungiyar Boko Haram abinci, a ci gaba da farautar 'yayan kungiyar da dakarun Najeriayr ke yi a yankin arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya kanal Sani Usman, ta ce, dakaraun kasar sun kama 'yayan kungiyar ne dauke da tarin abinci yayin da suka nufi yankin Damboa dake jahar Borno a lokacin da dakarun suka tsananta sintiri a yankin.

Sanarwa ta kara da cewer, ko da yake, wasu daga cikin wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewar su 'yan kasuwa ne, to sai dai ba su musanta yin huldar cinikayya da 'yayan kungiyar ba, amma a cewar sanarwar, ana ci gaba da gudanar da bincike.

Rundunar sojan Najeriyar ta ce, na samu nasarar tarwatsa sansanonin 'yayan kungiyar masu yawa a yankin, sa'annan ta lalata wasu tarin boma bomai da kungiyar ta daddasa a kauyen Sandia dake daura da Damboa.

Kazalika rundunar ta samu nasarar kubutar da mazaje da mata da kuma kananan yara wadanda 'yayan kungiyar ke tsare da su a yankin Bama da ke jihar Borno.

Da yake jawabi ga 'yan jaridu a Abuja, babban birnin kasar, mai magana da yawun hukumar tsaron kasar kanal Rabe Abubakar, ya ce, dakarun kasar suna samun galaba kan 'yayan kungiyar bayan kaddamar da aikin sintiri na hadin gwiwa tsakanin sojojin kasa da na sama a yankin Sambisa.

Da ma dai, shugaba Muhammadu Buhari na kasar, ya ba da umarni ga sojojin kasar da su murkushe kungiyar Boko Haram nan da watan Disamba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China