in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke wasu da ake zargi da samarwa 'yan Boko Haram katin shaidar zama 'dan kasa
2015-09-18 10:26:32 cri

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta cafke wasu mutane biyu, bisa zargin su da bugawa mayakan kungiyar Boko Haram katunan shaidar zama 'dan kasa na jabu.

Kakakin runduna ta 7 ta sojojin kasar mai helkwata a birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno kanar Tukur Gusau, shi ne ya tabbatar da kame mutanen. Ya kuma bayyana wa manema labaru cewa, hadin gwiwa tsakanin sojoji da sauran jami'an tsaron kasar, na haifar da gagarumar nasara ga kokarin da ake yi na kawo karshen ayyukan kungiyar.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin Makinta Umar, da John Zakariya ga manema labarai, kanar Gusau ya ce, an kame su ne bayan da wani 'dan Boko Haram ya toni asirin su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China