in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bayyana damuwa game da tsare shugaba Kafando
2015-09-17 09:24:18 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bayyana matukar rashin jin dadin, game da tsare shugaban gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso Mitchel Kafando, matakin da a cewar sa ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, da ma kudurin mika mulki ga zababbiyar gwamnati.

Rahotanni na cewa, dogaran fadar shugaba Kafando ne suka kutsa kai cikin dakin taro da shugaban ke yi da wasu mukarraban gwamnatin sa, suka kuma tisa keyarsa, shi da wasu kusoshin gwamnatin, ciki hadda firaministan kasar Yacouba Isaac Zida.

Game da hakan, babban magatakardar MDD ya bukaci jami'an tsaron da su gaggauta sakin Mr. Kafando, yana mai cewa. MDD, da ma al'ummar Burkina Faso na goyon bayan aniyar mika mulki ga zababbiyar gwamnati cikin lumana.

A wani ci gaban kuma, wakilin musamman na Mr. Ban a yammacin Afirka Mohamed Ibn Chambas, ya isa birnin Ouagadougou, domin tattaunawa da wakilan kungiyar ECOWAS, da sauran masu ruwa da tsaki game da batun tabbatar da nasarar shirin mika mulki ga zababbiyar gwamnati a kasar.

Yanzu haka dai kasa da wata guda ya rage a gudanar da babban zaben shugabancin kasar ta Burkina Fason, matakin da aka yi hasashen zai kawo karshen gwamnatin rikon kwaryar dake jagorancin kasar, tun bayan aukuwar tarzomar da ta kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Blaise Compaore.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China