Gwamnatin kasar Zimbabwe ta ce, tana da niyyar cire Sinawa masu bukatar ziyara daga cikin wadanda sai sun nemi visanta kamin su shiga kasar domin habaka bangaren yawon shakatawarta.
Ministan harkokin cikin gida Kembo Mohadi wanda ya tabbatar da hakan ya ce, kasar tana da wannan kuduri na daukaka Sinawa zuwa mataki na biyu a jerin wadanda kasar ta amince ma sai sun shiga kasar za su nemi takardar visa.
Ministan na magana ne a wani taron kara wa juna sani a kan sana'o'in Sinawa da mazauna yadda za'a shigar da su cikin kasar, taron da ma'aikatarsa ta shirya da hadin gwiwwar ofishin jakadancin kasar Sin a Zimbabwe.
A jawabinsa, jakadar kasar Sin a Zimbabwe Lin Lin ya ce, zai bi batun dage neman visan ga Sinawa sau da kafa domin ganin an cimma yarjejeniya cikin lokaci.
Sannan kuma jakadar ya yaba wa dangantakar abokantaka da ke wanzuwa tsakanin kasashen biyu, tare da lura da cinikayya ta dade tana wanzuwa tsakanin su cikin armashi, abin da ke karuwa da kashi 10 cikin 100 duk shekara. (Fatimah)