in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron Sin ya alkawarta karfafa dangantakar Sin da Zimbabwe
2015-03-27 10:14:04 cri

Ministan tsaron kasar Sin Chang Wanquan, ya alkawarta ci gaba da fadada dangantakar dake tsakanin kasarsa da Zimbabwe, musamman ma a fannonin tsaro da ayyukan soji.

Chang Wanquan ya bayyana hakan ne gabanin kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya gudanar a kasar ta Zimbabwe. Yayin ziyarar tasa, Mr. Chang ya zanta da mataimakin shugaban kasar Phelekezera Mphoko, da ministan tsaron kasar Sydney Sekeramayi. Sa'an nan ya kuma ziyarci kwalejin ayyukan tsaro dake wajen birnin Harare wadda kasar Sin ta gina.

Yayin da yake zantawa da mataimakin shugaban kasar, Mr. Chang ya jaddada cewa, kawancen dake tsakanin Sin da Zimbabwe na da dadadden tarihi. Ya ce, sama da shekaru 35 tun kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin sassan biyu, Sin da Zimbabwe sun baiwa juna goyon baya a fannoni daban daban.

Mr. Chang ya kara da cewa, yayin ziyarar aiki da shugaba Mugabe ya kai kasar Sin a bara, shi da shugaba Xi Jinping na kasar Sin sun daddale yarjejeniyar kara habaka dangantakar kasashen biyu.

A nasa bangare Mr. Mphoko, jinjinawa mahukuntan kasar Sin ya yi bisa goyon baya na tsahon lokaci da suka dade suna baiwa Zimbabwe, ciki hadda horas da ma'aikatanta, wanda hakan a cewar sa ya sanya Zimbabwe daukar kasar Sin a matsayin aminiya ta din din din. Daga nan sai ya yi fatan sassan biyu za su ci gaba da kokarin daga darajar dangantakarsu ya zuwa matsayi na gaba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China