in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya tsawaita wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau
2014-11-26 09:49:58 cri

Kwamitin tsaron MDD ya amince da tsawaita wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya a kasar Guinea-Bissau da watannin uku.

Bisa wannan mataki yanzu haka tawagar ta UNIOGBIS, za a ci gaba da ayyukanta a kasar har ya zuwa ranar 28 ga watan Fabarairun shekara mai zuwa.

Ana kuma fatan tawagar za ta ba da cikakkiyar gudummawa wajen taimakawa shirin tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki game da harkokin siyasar kasar, da fannin aiwatar da shawarwarin wanzar da zaman lafiya, tare da agazawa shirin dora kasar kan sahihiyar turbar dimokaradiyya.

A daya bangaren kuma kwamitin na tsaro ya bukaci mahukuntan kasar ta Guinea-Bissau da su zage damtse, wajen tabbatar da kare hakkokin bil'adama, da kare doka da oda, da kuma daukar matakan dakile aikata laifuka, ciki hadda hukunta masu keta hakkokin al'umma.

Bugu da kari kwamitin ya bukaci mahukuntan kasar da su yi nazari tare da daukar matakan aiwatar da managartan dokoki, da za su magance matsalar aikata manyan laifuka da ke shafar kasashe daban daban, musamman ma batun safarar miyagun kwayoyi, da kuma fidda kudade zuwa ketare ta barauniyar hanya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China