Kungiyar ECOWAS ta nada fitaccen 'dan siyasar nan na kasar Senegal Ibrahim Fall a matsayin manzon musamman na kungiyar da zai sasanta bangarorin da ke rikici a kasar Burkina Faso.
Kungiyar ta nada Ibrahim Fall ne kamar yadda dokokinta suka tanada yayin taron kolin shugabannin kasashe da gwamnatoci na kungiyar da aka gudanar a birnin Accra na kasar Ghana ranar 6 ga watan Nuwamba.
A wata sanarwa da kungiyar ta bayar ta bayyana cewa, Fall yana da kwarewa wajen sasanta rikicin siyasa a Afirka, sannan ya taba aiki a matsayin wakilin babban sakataren MDD mai kula da yankin Great Lakes, da manzon musamman na hukumar AU a kasar Guinea, sannan ya yi aiki a matsayin mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin siyasa.
Sanarwar ta kara da cewa, Fall ya taba rike mukamin shugaban tsangayar shari'a da tattalin arziki na jami'ar Cheik Anta Diop da ke Dakar, baya ga rike mukamin ministan harkokin wajen kasar ta Senegal.
Kungiyar tana ganin cewa, wadannan mukamai da jami'in ya rike za su taimaka masa wajen shawo kan sojojin kasar Burkina Faso su mika mulki ga hannun farar hula ba tare da bata lokaci ba, don ganin an maido da zaman lafiya da tsaro a kasar. (Ibrahim)