A wani jawabi ta gidan talabijin, sojojin sun bayyyana cewa, gwamnatin rikon kwaryar kasar da aka kafa na kokarin dora wanda take so a matsayin shugaban kasar, hakan a cewar su ba domekiradiyta ba ne.
Har yanzu ana zaman dar-dar a birnin Ouagadougou, tun bayan da sojojin suka yi awon gaba da shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Michel Kafando da firaministan kasar laftana kanar Yacoubu Isaac Zida da mukarraben gwamnatinsa.
An shafe daren jiya zuwa wayewar yau Alhamis ana ta jin karar harbe-harben bindiga, kana sojojin suna ta sintiri a kan tituna suna neman matasan da ba sa goyon bayan juyin mulkin.
Kungiyoyin fararen hula a kasar na yin kira ga jama'a da su yi zanga-zangar nuna adawa da juyin mulkin, yayin da ita ma kungiyar kwadagon kasar ta bukaci 'ya'yanta da su shiga yajin aikin sai baba ta gani a dukkan fadin kasar.
Gwamnatocin kasashen Faransa da Amurka da kungiyar tarayyar Afirka ta AU sun yi allah wadai da juyin mulkin da sojojin suka yi. (Ibrahim)