in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da sabon shugaban Mozambique
2015-01-16 10:06:30 cri

Zababben shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi, ya yi rantsuwar kama aiki, tare da alkawarin hade kan al'ummar kasar, da kuma dukufa wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin rantsuwar da aka gudanar a birnin Maputo, fadar gwamnatin kasar ta Mozambique a jiya Alhamis, shugaba Nyusi ya ce, gwamnatinsa za ta aiwatar da manufofi da za su zamo masu alfanu ga daukacin al'ummar kasar.

Ya ce, zai saurari shawarwari daga daukacin jama'ar Mozambique, tare kuma da ci gaba da ayyukan ginin kasa da ya gada daga shugaban kasar mai barin gado, musamman ma a fannonin raya ilimi, da samar da ababen more rayuwar jama'a.

Kaza lika a cewar shugaba Nyusi, gwamnatinsa za ta kara mai da hankali ga batun samar da ayyukan yi, da bunkasa sabbin sana'o'i, da inganta sha'anin noma da kiwo. Baya ga tabbatar da doka da oda, tare da rage kudaden da ake kashewa wajen gudanar da harkokin mulki. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China