in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta taya Burkina Faso murnar amincewa da kafa gwamnatin rikon kwarya
2014-11-18 09:44:06 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya taya al'ummar kasar Burkina Faso, murnar amincewa da dokar tabbatar da kafuwar gwamnatin rikon kwarya, tare da zabar sabon shugaba da zai jagoranci kasar ya zuwa lokacin gudanar babban zabe.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, babban magatakardar MDDr ya gode wa daukacin al'ummar kasar ta Burkina Faso bisa irin goyon bayan da suka bai wa shirin tattaunawar da ya gabata. Ya ce, yana sa ran ganin an kaddamar da sabon jagoran rikon kwaryar kasar, da sauran mambobin majalissarsa.

Kaza lika sanarwar ta bayyana aniyar MDD ta ci gaba da baiwa kasar tallafin da ya dace, a kokarin da ake yi na cimma nasarar mika mulki ga halastacciyar gwamnatin farar hula, bayan kammalar zaben kasar da ake fatan gudanarwa cikin watan Nuwambar shekarar badi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai masu ruwa da tsaki daga sassan kasar ta Burkina Faso suka amince da wani kuduri da ya tanaji tsara mika ragamar kasar ga zababbiyar gwamnati, bayan sojoji sun amshe iko na dan lokaci. Bugu da kari, kudurin ya tanaji mika ragamar kasar ga tsohon ministan harkokin waje Michel Kafando, a matsayin shugaban wucin gadi, ya zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zaben na shekara mai zuwa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China