Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya bukaci sabbin shugabannin da aka nada a kasar Burkina Faso da su yi aiki tare da juna, domin cimma muradun jama'ar kasar jiya Litinin.
Kakakin MDD Stephane Dujarric ya ce, magatakardan MDD ya yi kuma fatan za'a nada mambobin kwamitin wucin gadin kasar.
Burkina Faso ta yi shelar kafa sabuwar gwamnati a farkon wannan makon, a inda aka nada firaministan kasar kanal Isaac Zida a matsayin ministan tsaro.
Hakazalika, kamar yadda dokar kasar ta zayyana, shugaban kasar Michel Kafando shi ne ministan harkokin waje, dokar kasar ta kuma bayyana nadin wadansu ministoci 25 na ma'aikatun dabam-dabam na kasar ta Burkina Faso.
Magatakardan MDD ya bukaci daukacin kusoshin kasar da su magance dukannin wadansu al'amurra masu takaddama ta hanyar muhawara, domin tabbatar da samun nasarar gudanar da zabe a watan Nawumbar badi a cikin kwanciyar hankali da lumana. (Suwaiba)