A yayin da kasashen dake nahiyar Turai ke kokawar fidda kai daga tarin matsalolin tattalin arziki dake addabarsu, a hannu guda bankin bunkasa kasashen Afirka ADB, ya yi hasashen ci gaba da bunkasar nahiyar Afirka ta fuskar tattalin arziki cikin 'yan shekaru masu zuwa.
Wani rahoto da bankin ya fitar a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a ranar Laraba, ya nuna cewa, a bana, nahiyar za ta samu karin ci gaban tattalin arziki da kaso 4.8 cikin dari, yayin da a shekarar 2014, mizanin ci gaban zai karu zuwa kaso 5.3 cikin dari
A cewar babban jami'i a sashen nazarin tattalin arzikin bankin na ADB Mthuli Ncube, kasashen yammacin Afirka da suka hada da Saliyo, da Ivory Coast da Ghana, su ne za su zama a kan gaba, wajen karuwar tattalin arziki bisa ma'aunin GDP, a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2014.
Wannan matsayi, a cewar Ncube, zai sanya yankin yammacin Afirka, zama mafi samun ci gaba a wannan fanni, idan aka kwatanta da ragowar sassan nahiyar. (Saminu)