Ministan sadarwar kasar Mali, kana kakakin gwamnati, Choguel Kokalla Maiga ya gabatar wa 'yan jarida a ranar Labara da 'dan takarar Mali dake neman shugabancin bankin ci gaban Afrika (ADB), mista Birama Sidibe.
Zaben sabon shugaban bankin ADB, wanda kimanin kashi 60 cikin 100 na jarin bankin yake hannun kasashe 53, mambobin shiyyoyin da kuma kashi 40 cikin 100 tsakanin mambobi 26 da ba na shiyyoyin ba, zai gudana a yayin taron shekara shekara da zai gudana a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire daga ranar 25 zuwa 29 ga watan Mayun shekarar 2015.
Gwamnatin Mali ta samu goyon bayan kasashe goma sha daya dake wakiltar masu saka jari a bankin ADB, kuma shugaban kasar Mali tuni ya tuntubi takwarorinsa na kasashe mambobi na shiyyar Afrika na bankin ADB domin sanar da su da neman goyon bayansu ga 'dan takara Birama Sidibe, in ji ministan.
A cewarsa, mista Sidibe na da kwarewa, da hankali, da mutunci da gogewa domin rike wannan mukami. A cikin wannan aiki, za'a iyar cewa, mutum ne kuma kwararre na bankin ADB da muka sani, in ji kakakin gwamnatin kasar Mali.
Sauran 'yan takara bakwai dai dake neman shugabancin bankin ADB, sun hada da Akinwumi A. Adesina na Najeriya, Sufian Ahmed na Habasha, Jaloul Ayed na Tunisiya, Kordje Bedoumra na Chadi, Samura M.W.Kamara na Saliyo, Thomas Z.Sakala na Zimbabwe da kuma Cristina Duarte ta kasar Cap-Vert. (Maman Ada)