in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Afrika ya amince da kudin gyaran madatsar ruwan Zambiya da Zimbabwe
2014-12-18 10:01:10 cri

Bankin raya kasashen Afrika ADB ya amince da kudi dalar Amurka miliyan 75 domin gyaran madatsar ruwa mallakar Zambiya da Zimbabwe, kamar yadda jaridar Times ta Zambiya ta bayyana jiya Laraba.

Wakilin bankin a Zambiya Freddie Kwesiga ya ce, hukumar zartarwar bankin ta amince da kudin a ranar Litinin din wannan makon a matsayin bashi domin gyaran madatsar ruwan.

Hakan kuwa ya biyo bayan ziyarar Donald Kaberuka, shugaban bankin zuwa Zambiya a watan Yuli da kuma ziyarar hukumar zartarwar bankin zuwa Zambiyan da Zimbabwe har ma da ziyarar jakadun da manyan jami'an sauran kasashe zuwa madatsar ruwan ta Kariba.

Bankin ya yi alkawarin samar da kudin domin gyaran madatsar ruwan saboda ban da zama mai muhimmanci ga kasashen biyu, madatsar ruwan tana da amfani ga sauran kasashe dake yankin.

Madatsar ruwan Kariba, ita ce mafi girmar tabkin da aka kafa a nahiyar Afrika, kuma tana daf da wargajewa idan har ba'a dauki matakan gaggauwa na gyara bangonta da ya tsatsage ba.

Tsakanin shekara ta 1956 da 1959, madatsar ruwan ita take samar da kashi 50 cikin dari na lantarkin da kasashen biyu na Zimbabwe da Zambiya ke amfani da ita ga al'ummomi miliyan 4.5. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China