in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Abbas ya bukaci a mayar da Palastinawa matsugunansu
2015-09-06 11:16:22 cri

Shugaban al'ummar Palastinawa Mahmoud Abbas ya yi kira ga jakadansa dake MDD da ya dauki matakan gaggawa domin sake mayar da Palastinawa 'yan gudun hijira muhallansu a yammacin gabar kogin Jordan.

A wata sanarwa daga ofishin shugaban Palastinawan ya rawaito cewar, tuni shugaba Abbas ya fara tuntubar ofishin MDD da kungiyar tarayyar Turai wato EU da sauran hukumomin duniya da su yi matsin lamba ga gwamnatin Isra'ila da ta tabbatar an baiwa al'ummar Palstinawa dake gudun hijira damar sake komawa matsugunansu dake yammacin gabar kogin Jordan.

Shugaba Abbas ya ce, wannan mataki na sake mayar da al'ummar Palastinawa muhallansu zai kawo karshen mace macen da Palastinwa 'yan gudun hijira ke fuskanta sakomakon mawuyacin halin da suka shiga sabo da mamayar da Yahudawa 'yan kama guri zauna ke yi musu, musamman 'yan gudun hijirar da rikicin ya tillastawa tsallakawa zuwa Syria kawacce ke fama da rikici.

Bugu da kari kungiyar fafutukar 'yancin al'ummar Palastinawa wato PLO a takaice ta yi kira ga gwamnatin Syria da ta baiwa 'yan gudun hijarar Palastinu kyakkyawar kulawa domin kada su tsallaka zuwa kasashen Turai.

Mamban kwamitin gudanarwar kungiyar ta PLO Ahmed Majdalani ya sheidawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a ranar Asabar din nan cewar, akwai matukar fargaba ga 'yan gudun hijirar dake tsallakawa Turai sakamakon hasarar daruruwan rayukan da ake fuskanta a kokarin haurawa kasashen Turai.

Kimanin Palastinawa 'yan gudun hijira dubu 3 ne suka hallaka a sanadiyyar rikicin kasar Syria, kuma adadin Palastinawa dake gudun hijira a Syria ya kai dubu 200, haka zalika yawan Palastinawan da mamayar Yahudawa ta tilastawa kaucewa matsugunansu ya zarta dubu 700 a halin yanzu. (Ahamd Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China