in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya bukaci a baiwa fararen hula damar jagorantar shirin mika mulki a Burkina Faso
2014-11-05 13:56:21 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bukaci da a baiwa fararen hula cikakkiyar damar jagorantar gwamnatin rikon kwarya, tare da shirin mika mulki ga zababbiyar gwamnati a Burkina Faso.

A cewar kakakinsa Farhan Haq, tuni wakilan Mr. Ban suka gana da sassan masu ruwa da tsaki, a kokarin da ake yi na tabbatar da hakan. Haq wanda ya bayyana wa taron manema labaru hakan ya ce, a ranar Litinin, wakilan MDD da hadin gwiwar tawagar wakilan kungiyar ECOWAS, sun gana da shugaba John Mahama na Ghana, domin tattaunawa game da halin da ake ciki a kasar ta Burkina Fason.

Kaza lika wakilin babban magatakardar MDD a Afirka ta yamma Mohammed Ibn Chambas, ya yi wa shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe karin haske game da yanayin da ake ciki.

Chambas ya ce, daukacin masu ruwa da tsaki sun amince da bin dokokin dake shinfide cikin kundin mulkin kasa ta Burkina Fasa, a matsayin sahihiyar hanyar maida kasar kan turba mafi dacewa.

Yanzu haka dai tawagar masu ruwa da tsakin ta koma birnin Ouagadougou, domin ganawa da karin masu ruwa da tsaki, a ci gaba da kokarin aiwatar da burin mika mulki ga zababbiyar gwamnati karkashin kulawar fararen hula. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China