in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe mayakan Boko Haram 24 a arewacin Kamaru
2015-07-08 09:51:08 cri

A kalla mayakan kungiyar Boko Haram ta Najeriya 24 aka kashe a yayin da suka kai wani hari a sansanin soja da ke kuriyar arewacin kasar Kamaru a ranar Talata da safe, a cewar wani adadin da ba a tabbatar ba, da wasu majiyoyin tsaron kasar suka bayar.

Wani gungun mayakan Boko Haram ya shiga kasar Kamaru da misalin karfe uku na dare bisa agogon wurin, kana ya dauki hanyar Bodo, wani garin da ke kusa da iyaka da Najeriya, inda ya yi yunkurin kai harin ba zata kan sansanin sojojin musamman na rundunar sojojin Kamaru, a cewar wadannan majiyoyi. Da yake suna cikin shirin ko ta kwana, sojojin Kamaru sun mai da martani ta hanyar barin wuta kan maharan na Boko Haram. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China