in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin filin jirgin Karachi ya janyo asarar rayuka da dama
2014-06-09 10:15:44 cri

Mahukuntan kasar Pakistan sun ce, harin da wasu 'yan bindiga suka kai filin tashi da saukar jiragen sama dake Karachi, a daren ranar Lahadi ya janyo asarar rayuka da dama.

A cewar kakakin rundunar sojin kasar Manjo Janar Asim Bajwa, dukkanin 'yan bindigar 10 sun rasa rayukan su, yayin musayar wuta da ta auku tsakanin su da jami'an tsaro, biyowa bayan harin da suka kai wasu sassa na filin jirgin.

Kafofin yada labarun kasar dai sun ce, tun da fari 'yan bindigar sun kutsa filin jirgin saman na Jinnah ne, ta sashin da ake ajiye jiragen dakon kaya, suka kuma budewa jami'an tsaron dake sashen wuta, kafin daga bisani su kunnawa wasu jiragen kasashen ketare biyu wuta. Kaza lika maharan sun cinna wuta a wani sashi na ajiyar mai dake filin jirgin, ko da yake dai mahukuntan kasar sun musanta batun kone jiragen.

Bugu da kari, wata majiyar gidan talabijin dake kasar, ta bayyana cewa, wasu mutane su 10, da suka hada da ma'aikatan tsaron filin jirgin 7, da 'dan sanda daya, da wani ma'aikacin hukumar lura da sifirin jirage da kuma wani soja guda, na cikin wadanda suka rasa rayukan su yayin bata-kashin da ya auku. Baya ga kuma wasu jami'an tsaron su 18 da suka samu raunuka sakamakon harin.

An dai dakatar da zirga-zirgar jirage bayan aukuwar wannan balahira, yayin da kuma firaministan kasar Nawaz Sharif ya umarci rundunar jami'an tsaron kasar da ta kara azamar kare rayukan fararen hula.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China