Fiye da kananan yara 1070 ake ganin suke da alaka da kungiyoyi masu maikamai, a cewar wani bincike na reshen kare yara kanana na tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Congo DRC (MONUSCO) na shekarar 2015, in ji Felix Basse, kakakin farar hula na wannan tawaga a yayin wani taron manema labarai na MDD a ranar Laraba a birnin Kinshasa.
Halin da ake ciki shi ne yaran da ke son tserewa daga hannun kungiyoyi masu makamai a yayin ayyuka da yake yake na ci gaba da karuwa. A tsawon makwanni biyu na baya bayan nan, yara kusan 100 aka raba su da kungiyoyi masu makamai, a Arewacin Kivu, kamar kungiyar FDLR, da kungiyar NDC ta shugaban mayakan Cheka, in ji mista Basse, tare da kara cewa, zaman rayuwar yaro daya a cikin wata kungiyar mai makamai wata babbar azaba ce, in ji MONUSCO. (Maman Ada)