Gwamnatin DRC-Congo ta kimanta bukatar majalisar tarayyar Turai na sako masu rajin kare hakkin dan adam na Filimbi, wata kungiyar 'yan kasar Congo, a matsayin wani shisshigin da ba za a amince da shi ba.
Gwamnati ta yi watsi da wannan shisshigin da ba za a amince da shi ba a cikin harkokin cikin gida na DRC daga wasu abokan hulda na kasashen waje da ke amfani da wani matsayin da ba shi cikin dokokin kasa da kasa, ko a cikin dokokin kasar Congo, in ji ministan watsa labarai kuma kakakin gwamnati, Lambert Mende, a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar.
Gwamnati na tunatar tare da babbar murya cewa, majalisar tarayyar Turai ba ta da 'yancin yin katse lamda ga hukumomin wata kasar Afrika mai 'yanci kamar DRC-Congo, in ji kakakin.
Ana zargin mambobin Filimbi biyun da shiga cikin wata kungiyar da ke da hannu wajen tozarta shugabannin kasashen Afrika, da rura wutar gaba da tashe tashen hankali, da rura wutar kabilanci, da kuma yayata miyagun ayyuka, musammun ma yin kira ga yi wa matan wasu kabilu fyade ta hanyar tura sakwanni a kan shafukan internet. (Maman Ada)