in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Mali na ziyarar aiki a Algeria
2015-08-31 09:38:45 cri

Shugaba Ibrahim Boubacar Keita na kasar Mali, ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Aljeriya tun daga jiya Lahadi, a wani mataki na bunkasa huldar diflomasiyyar kasashen biyu, bisa gayyatar shugaban Algeriyan Abdelaziz Bouteflika. Tuni dai kakakin majalissar wakilan kasar Aljeriya Larbi Ould Khelifa ya tarbi shugaba Keita a filin tashi da saukar jiragen saman birnin Algiers.

A cewar kamfanin dillancin labaru na APS, fadar shugaban kasar Mali na fatan wannan ziyara za ta karfafa huldar kawance, da makwaftaka dake tsakanin kasashen biyu. Kana shugabannin kasashen za su yi amfani da ita wajen tattauna batutuwan da suka jibanci yankinsu, da ma sauran al'amura na kasa da kasa.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu dai na kara habaka a 'yan shekarun baya bayan nan, musamman ma tun bayan da Algeria ta jagoranci shirin kasa da kasa na shiga tsakani a rikicin siyasar kasar Mali. Algeria ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar shawarwarin wanzar da zaman lafiya a Mali cikin shekaru kusan 2 din da suka gabata, matakin da ya kai ga rattaba hannu kan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da sasanto ta watan Mayun da ya shude.

Bugu da kari kasashen biyu sun kafa wani kwamitin tuntuba na hadin gwiwa, wanda zai bibiyi yadda ake aiwatar da manufofin wanzar da zaman lafiya da yafiya a arewacin kasar ta Mali. A daya hannun kuma sassan biyu sun amince da hada karfi da karfe wajen yaki da ta'addanci, da kare kan iyakokinsu, da kuma bunkasa ci gaban yakunan dake daura da kan iyakokin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China