in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Algeriya sun kame 'yan sumogal 110 kan iyakar kasar da Niger
2015-08-25 09:45:20 cri

Sojojin kasar Algeriya sun kame 'yan sumogal 110 a kan iyakar kasar kamar yadda majiyar sojin ta tabbatar.

Adadi mafi yawa na kame 'yan sumogal 110, an yi shi ne a kauyukan garin Tirinine dake kan iyakar kasar da jamhuriyar Niger, inda sojojin suka kame manyan motocin dauke da na'urorin tantance karafa 58, jackhammer 15, injin din janarato 2, na'urar TNT mai nauyin giram 608, wayar salula 4, sikeli da kudin sefa 45,000.

Mahukuntar Algeriya sun ce, wannan ayari sun nufi daya daga cikin mahakan zinari ne a cikin sahara wanda har yanzu ba'a fara hakar shi ba a hukumance.

An kara damke wasu 'yan sumogal guda 4 a kan iyakokin kasar ta gabas, yamma da kuma kudu, inda aka kwace kayayyaki da dama da suka hada da mai, magunguna, kamarorin nuna hoton wuri, na'urar tantance bayanai da wurare ta GPS.

Bayan kara yawan sojoji a kan iyakokin kasar domin tare shigowar 'yan ta'adda, musamman ma daga kasashen Libya, Tunisiya da Mali, sojojin suna bankado ayyukan sumoga a kusan duk rana da gungun miyagu ke aiwatarwa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China