in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya yi maraba da taron sasanta rikicin siyasar Libya
2015-07-02 09:50:23 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya yi maraba da taron sasanta rikicin kasar Libya da ya gudana a kasar Morocco daga ranar 25-28 ga watan Yuni.

Cikin wata sanarwa da kwamitin ya rabawa manema labarai, kwamitin ya sake nanata kudurin sa cewa, matakin soji ba zai taba magance matsalar kasar ta Libya ba, don haka ya bukaci mahalarta taron da su amince da shirin kafa gwamnatin hadaka, kana su amince da shawarar da tawagar MDD da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Libya (UNSMIL) ta gabatar cikin kwanaki masu zuwa.

Kwamitin sulhun ya ce, ya yaba da kokarin mahalarta taron warware matsalar siyasar kasar, da ma ragowar matakan samar da zaman lafiya, ciki har da gudummawar da kungiyoyin fararen hula suka ba da, tsagaida bude wuta a matakin kasa, musayar fursunoni, kana da maido da mutanen da rikicin ya raba da gidajensu.

MDD dai ta sha shirya tarukan sasantawa tsakanin bangarorin da ke gaba da juna a kasar ta Libya, amma ana ci gaba da gwabza fada duk da yarjejeniyar da bangarorin suka cimma a tsakaninsu. Kasar Libya ta tsinke kanta cikin rikicin siyasa ne tun bayan da boren siyasar kasar na shekarar 2011 ya yi awon gaba da tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China