Rundunar 'yan sanda a kasar Uganda ta ce, ta yi shirin ko ta kwana game da wani faifan bidiyo da ake zargin 'yan mayakan Somaliya na Al-Shabaab ne suka aike da shi ta kafar sadarwa ta YouTube, inda suka yi kiran da a fito a yi jihadi ta hanyar kai hari a Uganda da kuma Burundi.
A cikin wata sanarwar, rundunar 'yan sandan ta ce, sakon da aka fitar a ranar Alhamis din nan, faifain bidiyo na tsawon mintuna 12 da aka fitar ranar Litinin din wannan makon yana da lakabin "sako na karshe na jaruman Kamfala" ba abu ne da za' a yi sakaci da shi ba, don haka rundunar ta 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro suna mai da hankali wajen kara tantance bidiyon da kuma sahihanci na kafar da aka aika da shi, in ji sanarwa.
Sanarwar ta ce, sanin kowa ne cewa barazanar ta'addanci ko da gaske ko da wasa, zai yiwu an shirya shi, don haka daukacin hukumomin tsaro suna ci gaba da hada bayanan da suka wajaba daga jama'a.
Kasar Uganda dai tana ci gaba da samun barazanar ta'addanci daga kungiyar Al-Qaida da suke da alaka da kungiyar Al-Shabaab na Somaliya, saboda taimakon sojojin ta da ta aike domin kwato Somliyan daga hannun 'yan ta'addan.
Ita ce kasa mafi yawan rundunar soji a cikin sojojin kiyaye zaman lafiya karkashin kungiyar tarayyar kasashen Afrika ta AU. Kungiyar Al-Shabaab a watan Yuli na shekara ta 2010 ta kai tagwayen hare hare da suka hallaka mutane 76, sannan da dama suka ji rauni a babban birnin kasar Kamfala. (Fatimah)