in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan sandan Ugandan ta fitar da gargadi game da harin ta'addanci
2015-06-23 09:29:07 cri

Rundunar 'yan sanda a Uganda a ranar Litinin din nan ta fitar da wani gargadi da mayakan Al-Shabaab na kasar Somaliya suka aika na shirin kai harin ta'addanci a wurare daban daban a wannan wata mai muhimmanci ga musulmai na Ramadan.

Fred Enanga, kakakin 'yan sandan ya shaida wa Xinhua cewa, hukumomin tsaro sun samu bayanan sirri da suka bayyana shirin mayakan na Al-Shabaab na kai hari a Somaliya, Uganda, Kenya da kuma Habasha a cikin wannan lokaci na azumi.

Gargadin dai ya zo ne kasa da kwana daya bayan da wata mota mai dauke da bam ta tashi, sannan wassu masu dauke da makamai suka far wa cibiyar horon jami'an leken asiri ta kasar Somaliya dake Mogadishu a ranar Lahadin nan da ta gabata. Kasar dake kudancin Afrika ta ba da mafi yawan jami'an tsaro a karkashin shirin kungiyar tarayyar kasashen Afrika ta AU domin yakar 'yan ta'addan tun daga shekara ta 2007.

A ranar 11 ga watan Yulin shekara ta 2010, kungiyar ta Al-Shabaab ta aiwatar da tagwayen hare hare da suka hallaka fiye da mutane 76, da wassu masu tarin yawa da suka tsira da raunuka a Kampala, babban birnin kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China