Wata majiya daga gwamnatin Somaliya ta ce, dakarun kasar tare da hadin gwiwar sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar hada kan kasashen Afrika AU sun samu nasarar sake kwace ikon kauyen Halgan dake yankin Hiran na tsakiyar Somaliya daga mayakan Al-shabaab.
Babban jami'i mai kula da gundumar Halgan Mustaf Herow Nor, ya tabbatarwa manema labarai cewar, dakarun na hadin gwiwa sun samu nasarar sake kwace ikon kauyen ne a ranar Litinin din nan ba tare da fuskantar turjiya daga mayakan na Al-shaabab ba.
Ya kara da cewar, dama tun tuni mayakan na Al-shabaab sun fice daga kauyen kafin isowar dakarun hadin gwiwar, sai dai har yanzu dakarun na ci gaba da yin sintiri domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Jami'an gwamnatin kasar sun tabbatar da cewar, sun kwance nakiyoyi masu yawan gaske da mayakan na Al-shabaab suka daddasa a kan hanyar kauyen kafin ficewarsu.
Wasu mazauna kauyen sun sheda wa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ta wayar hannu cewar, dakarun gwamnatin dauke da makamai sun kwace ikon kauyen ne cikin ruwan sanyi.
A cewar wani mazaunin kauyen Abshir Ahmed, garin na cikin kwanciyar hankali a halin yanzu, kuma dakarun gwamnatin kasar na ci gaba da aikin wanzar da zaman lafiya. (Ahmad Fagam)