Samar da zinari da kasar Sudan take yi ya kai tan 54 a cikin watanni 8 da suka gabata tsakanin kamfanoni masu aiki da hanyar gargajiya da na zamani, a cewar ministan ma'adinan kasar Ahmed Mohammed Sadiq Al-karouri, a zantawar da ya yi da manema labarai a birnin Khartoum. Ahmed Mohammed Sadiq Al-karouri ya ce. an samu karuwar samar da zinarin da sauran ma'adinai kwarai da gaske, musamman a bangaren kamfanonin hakowan wadanda suka shiga matakin sarrafa shi domin ba da gudunmuwa wajen farfado da tattalin arzikin kasar da rabuwar ta da kasar Sudan ta Kudu ya kawo mata hakan.
Sudan dai ita ce kasa ta 3 a nahiyar Afrika wajen samar da zinari bayan kasashen Afrika ta Kudu da Ghana, abin da masu sa ido ke hasashen za ta iya kaiwa matakin farko a shekara ta 2018.
Adadin kudin shiga da zinarin ke samarwa kasar ya wuce dalar Amurka biliyan daya a shekarar bara ta 2014 wanda ya samar da tan 71.(Fatimah)