in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yunkurin samun zaman lafiya a Rwanda ya samu ci gaba
2015-09-01 09:45:31 cri

Kasar Rwanda ta yi kokari domin ganin ba'a maimaita fadan da ya taba aukuwa na kisan kare dangi ba, in ji Donatille Mukabalisa, kakakin 'yan majalisar dokokin Rwanda a ranar Litinin lokacin babban taron duniya na shugabannin majalissun dokoki karo na 4.

Madam Donatille Mukabalisa ta ce, sake gina kasar Rwanda domin tabbatar da dawwamamen zaman lafiya da tsaro yana bukatar sadaukarwa sosai, musamman ganin yadda ta yi fama da yaki da ya haifar da kisan kare dangi a shekara ta 1994, wanda a cikin mutane 7 aka hallaka mutum 1 cikin kwanaki 100.

Madam Mukabalisa ta ce, Rwanda tana bukatar samar da yanayi na zaman lafiya da karko ga kowa da kowa, a sake gina gwamnati da za ta inganta tattalin arziki da ci gaban zamantakewar jama'ar kasar.

Ta ce, ana bukatar matukar sadaukar da kai daga 'yan kasar a cikin wannan aiki na sake gina kasa, ba abu ne da zai faru dare daya ba.

Ta lura cewa, ganin yadda kasar ta Rwanda ta yi kokari tukuru na sake kafa gwamnati, yanzu tana iya taimakawa sauran kasashe da ya hada da ba da gudunmuwa na sojoji zuwa ga ayyukan zaman lafiya na MDD. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China