Masana a fannin tattalin arziki na cewa, faduwar darajar mai a kasuwannin duniya, ta haifar wa Najeriya koma baya, matakin da zai kai ga daukar matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin kasar.
Wani masani a fannin tattalin arziki a Najeriyar Tope Fasua, ya bayyana wa majiyarmu cewa, a baya, an yi hasashen cewa, ma'aunin bunkasar tattalin arzikin kasar na GDP na iya karuwa zuwa kaso 6.8, ko kaso 7 bisa dari, amma tafiyar hawainiyar da sashen na tattalin arziki ke fuskanta a yanzu haka zai wajibta sake duba wannan hasashe.
Fasua ya kara da cewa, manufar tsuke bakin aljihu na nufin tattalin arzikin kasar ya shiga matsala, wanda kuma hakan ke nuna wajibcin tunkarar wannan kalubale ta hanyar daukar wasu matakai masu yawa.
A watan da ya gabata ne dai mahukuntan kasar suka rage dala 5 kan ko wace gangar mai, cikin kasafin kudin kasar na badi, bayan da farashin danyan mai ya sauko daga dala 78 zuwa dala 73 kan ko wace ganga. Har wa yau gwamnatin kasar ta sanar da fara aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu, da nufin rage tasirin faduwar darajar man.
Game da hakan ministan kudin kasar Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce, ko da yake faduwar farashin mai babban kalubale ne ga kasar, a hannu guda hakan zai sanya kasar karkata tunai ga sauran sassan da ba na mai ba, wajen samar da kudaden shiga. (Saminu)