in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude wani dandalin musanya tsakanin Sin da Afrika a Afrika ta Kudu
2015-09-10 11:10:30 cri
Dandalin musanya tsakanin Sin da Afrika (CATTF) karo na hudu ya bude kofa a ranar Labara a birnin Pretoria na kasar Afrika ta Kudu tare da yin kira ga karfafa huldar dangantaka.

CATTF, wani shiri ne da jami'ar Zhejiang (ZJNU) ta kaddamar a shekarar 2011 domin kafa wani tsarin tuntubar juna da yin musanya tsakanin manazartan Sin da Afrika.

Da yake jawabi ga mahalarta a yayin bude taron, forfesa Jiang Guojun, shugaban jami'ar ZJNU, ya bayyana cewa taron na kwanaki biyu zai mai da hankali kan hanyoyin karfafa dabarun cigaba na Sin da Afrika, moriyarsu da hakikanin halin da suke ciki.

A nata jawabi, jakada Mxakatho Diseko, mataimakiyar darekta janar ta ma'aikatar harkokin wajen Afrika ta Kudu, ta yi kira ga mambobin CATTF da su bullo da dabarun da za su taimakawa Sin da Afrika domin wuce kalubalolin da ke gabansu.

Inda ta kara da cewa Sin da Afrika suna cigaba da taka muhimmiyar rawa kan tattalin arzikin duniya. A cewarta, Sin da Afrika suna rike a cikin hannayensu da taswirar sake farfado da cigaban duniya mai dorewa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China