Darektan tabbatar da amfani da doka da samar da horo na ofishin kare namun dajin da ke fuskantar barazanar karewa a duniya na sashin kula da gandun daji na majalisar gudanarwar kasar Sin Wan Ziming ne ya bayyana hakan, yayin zaman samun horo game da yadda za a kare fataucin namun daji ba bisa doka ba a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.
Ya ce kasar Sin, mamba ce ta kasashen da suka sanya hannun ka yarjejeniyar kasa da kasa da ta haramta fataucin namun daji ba bisa ka'ida ba. Don haka, gwamnatin kasar Sin tana goyon bayan kamfel din da ake yi na haramta farautar giwaye da karkanda a Afirka.
Darektan ya kara da cewa, suma ofisoshin jakadancin kasar Sin da kamfanoninta da ke gudanar da ayyukansu a Afirka, za su shiga a dama da su a kemfel din da ake yi.
Kwararru kan kare namun daji, sun lura da cewa, kasar Sin tana da tasiri sosai Afirka, kuma za ya iya samar da tallafin kudi da kwarewa a kokarin da ake yi na yaki da farautar namun dajin. (Ibrahim Yaya)