in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan gudun hijirar Najeriya 11000 na cikin mawuyacin hali a Chadi
2015-01-15 10:50:53 cri

Mutane fiye da 11000 da suka gujewa hare hare da tashe tashen hankalin kungiyar Boko Haram a kasar Najeriya, domin samun mafaka a kasar Chadi makwabciyar Najeriya, suna cikin mawuyacin hali, a cewar kungiyoyin bada agaji.

A tsawon ranakun farko na shekarar 2015, kusan mutane 7300 suka gujewa hare haren da kungiyar Boko Haram ta kai a kauyukan dake kan iyaka a arewacin Najeriya, musammun ma a Baga, domin samun mafaka a yammacin Chadi, a cewar wani rahoton farko kan wannan matsala da cibiyar kula da harkokin jin kai ta MDD dake kasar Chadi ta fitar a farkon mako.

Wasu majiyoyin jin kai sun jaddada cewa, yawancin masu zuwan mata ne da yara, domin ana zaton mazan an kashe su ko an raba su da iyalensu a lokacin hare hare, ko ma lokacin da suke kaura daga muhallinsu.

Haka kuma akwai yara 89 da ba su tare da 'yan rakiya, a cewar UNICEF. Gaban wannan matsala ta kwarar 'yan gudun hijiran Najeriya a yankin tafkin Chadi, gamayyar kasa da kasa na da wajabcin nuna goyon baya da raba aiki, tare da daukar nauyin dake wuyansu.

Idan ba mu dauki matakai cikin lokaci ba, za mu shiga cikin matsalar da za ta fi karfinmu, in ji rahoton. Shugaban gwamnatin Chadi ya bayyana niyyarsa na bude wani sassanin 'yan gudun hijira a yankin tafkin Chadi, domin tabbatar da tsaro da ba da agaji ga mutanen da suka fito daga Najeriya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China