Game da hakan, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya bayyana cewa jawabin da shugaba Xi ya gabatar na nuna cewa Sin za ta kokarta wajen aiwatar da manufar samun ci gaba cikin lumana, kuma Rasha ta jinjinawa wannan mataki.
A nasa bangare, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya fidda wata sanarwa dake cewa wannan biki ya nuna cewa, Sin za ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da duk sauran kasashen duniya. A matsayin wata babbar kasa, Sin ta aiwatar da matakan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, ba kuma tare da kai hari kan sauran kasashen duniya ba.
Bugu da kari Jacob Zuma ya bayyana cewa, Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen 'yantar da kasashen Afirka, tare da ba da taimako mai dimbin yawa. Ya ce akwai dankon zumunci tsakanin Sin da kasashen Afirka cikin dogon lokaci. Har wa yau a yanzu dangantaka tsakanin sassan biyu ta shiga wani sabon mataki, inda bangarorin biyu ke kokarin gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu, domin sa kaimi ga raya masana'antu, da samar da manyan ababen jin dadin jama'a a kasashen Afirka.