Wani masanin kasar Sin dake aiki a kwalejin nazari kan dangantakar kasashen duniya dake Nijeriya, ya bayyana cewa, Sin ba ta taba tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasashen Afirka ba. A maimakon haka, ta kan ba da ainihin gudummawa bisa yanayin da ake ciki, domin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da kyautata rayuwar jama'a. Bugu da kari, Sin ta rika jaddada cewa, bunkasuwa za ta ba da tabbaci ga samun zaman lafiya, haka kuma tabbatar da zaman lafiya zai samar da yanayi mai kyau ga samun bunkasuwa. A sabili da haka, bunkasuwar Sin ta ba da gudummawa ga tabbatar da zaman lafiya a duniya, tare da kawo zarafi mai kyau ga kasashen Afirka a wannan fanni. (Fatima)