Lauya Benewende Sankara na kawancen jam'iyyun UNIR da PS, 'dan takatar zaben shugaban kasar Burkina-Faso na ranar 11 ga watan Oktoba mai zuwa, ya bukaci da a soke takarar wasu mutane hudu na kusa da hanbararren shugaba Blaise Compaore, da yake zarginsu da goyon baya wajen yi wa kudin tsarin mulki gyara fuska domin sake baiwa Compaore damar sake neman wani wa'adin mulki.
Lauya Benewende Sankara ya shigar da wannan bukata a ranar Asabar a gaban kotun tsarin mulki kan zargin Djibril Yipene Bassole, tsohon shugaban diplomasiyya na Compaore, Yacouba Ouedraogo, tsohon ministan wasannin motsa jiki, da kuma Ram Ouedraogo da Salvador Yameogo, dukkansu jami'an siyasa na tsohon gungun masu rinjaye a karkashin jagorancin jam'iyyar kishin kasa mai mulki a lokacin. (Maman Ada)