Babbar kotun tsara dokokin kasar Burkina-Faso ta gabatar da takardar wucin gadi ta sunayen 'yan takarar zaben shugaban kasar na ranar 11 ga watan Oktoban shekarar 2015, inda ta rike 16 daga cikin 'yan takara 22, a cewar wata sanarwar wannan babbar hukuma a ranar Lahadi. Daga cikin 'yan takara goma sha shida, akwai mata biyu.
Kuma wannan shi ne karon farko da aka samu mata da za su shiga takarar zaben shugaban kasa a Burkina-Faso. Haka kuma kotun ta janye takarar mutane shida, har da wasu mutane biyu na kusa da tsohon shugaban kasar Blaise Compaore. (Maman Ada)