Gwamnatin Burkina Faso ta nuna yabo a ranar Alhamis ga shugaban kasar Najeriya mai barin gado Goodluck Jonathan bisa amincewa da faduwarsa a zaben shuagban kasa, wanda janar Muhammadu Buhari ya lashe a ranar Asabar da ta gabata, a cewar wata sanarwa ta gwamnatin kasar.
Gwamnatin wucin gadin Burkina Faso ta taya murna ga Muhammadu Buhari, tare da yaba da dattakun Goodluck Jonathan bisa amincewa da nasarar abokin takararsa.
A cewar sabbin hukumomin kasar Burkina Faso da suka fito daga boren al'ummar kasar da ya kifar da mulkin shugaba Blaise Compaore a cikin watan Oktoban shekarar 2014, wannan karfi da fatan 'yan Najeriya suka bayyana ya kawo kwarin gwiwa ga zabin al'ummar kasa, kuma ya kasance wani babban misali ga kafuwar demokaradiyya.
Gwamnatin Burkina Faso ta kuma yaba da yadda wannan zaben tarihi da ke bayyana canji cikin lumana da kuma kasancewa wani muhimmin mataki a cikin tarihin siyasar Najeriya da ke fama da masu kaifin kishin addinai. (Maman Ada)