in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin hanci ya zama ruwan dare a idon kashi 91 cikin 100 na al'ummar Burkina Faso
2015-07-02 11:10:11 cri

Kashi 91 cikin 100 na al'ummar kasar Burkina Faso na ganin cewa, cin hanci ya zama ruwan dare ko ma a ce ya kazanta a cikin kasarsu, a cewar wani rahoton baya baya kan matsayin cikin cin hanci a kasar Burkina Faso da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar (REN-LAC) ta fitar a ranar Talata.

A cewar wannan bincike da aka gudanar bisa rukunin mutane dubu biyu wanda daga cikinsu kashi 49,5 cikin 100 mata ne, kuma kashi 74 cikin 100 da aka yi bincike kan su sun yi karatu, matsalar cin hanci na ci gaba da karuwa, a cewar yawancin mutanen da aka bincika wato kashi 42 cikin 100 na wadanda suka ba da amsa, haka kuma hanyoyin cin hanci sun karu idan aka kwatanta da na shekarar 2013. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China