Kasar Afrika ta Kudu ta kara lokacin jibge sojojinta har zuwa shekara daya a jamhuriyyar demokaradiyar Congo (DRC-Congo), Sudan da cikin kasashen kungiyar raya kudancin Afrika, in ji fadar shugaban kasar a ranar Talata.
An kara lokacin jibge sojoji 1388 a kasar DRC-Congo da kuma sojoji 850 a yankin Darfur na kasar Sudan, zuwa shekara daya wato har zuwa 31 ga watan Maris na shekarar 2016, in ji kakakin fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu, mista Mac Maharaj.
Wadannan rukunonin sojoji dukkansu suna halartar aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar DRC-Congo da ta tawagar zaman lafiya ta hadin gwiwa ta MDD da tarayyar Afrika (AU) a yankin Darfur.
Rukunin sojojin 220 da aka tura a cikin tawagar ladabtarwa ta yaki da fashin teku da wasu sauran ayyukan da suke sabawa doka a tsawon iyakokin ruwan kasar Afrika ta Kudu a kan tekun Indiya shi ma an kara wa'adinsa har zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2016. (Maman Ada)