in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda za ta rike shugabancin kwamitin tsaron MDD a watan Yuli
2014-07-02 10:36:50 cri

Kasar Rwanda, aka azama a wannan ranar Talata nauyin jagorantar kwamitin tsaro na MDD a wannan karo, aikin da kasar za ta cigaba da rikewa har tsawon watan Juli.

Mista Eugene-Richard Gasana, wakilin din din din na kasar Rwanda a MDD, ya maye gurbin jakadan kasar Rasha a MDD, mista Vitali Tchourkine domin kasancewa shugaban kwamitin tsaro.

Bisa jadawalin aiki na wucin gadi da kwamitin tsaron na MDD ya tsara bisa tsawon wata Yuli, mambobi goma sha biyar na kwamitin za su yi taro domin gudanar da muhawara bisa babban mataki kan dangantakar yankunan dake nasaba da ayyukan tabbatar da zaman lafiya na MDD, muhawarar da ministar harkokin wajen kasar Rwanda, madam Louise Mushikiwabo za ta jagoranta.

Muhawarar watanni uku kan Gabas ta Tsakiya na cikin jadawalin wannan watan, tare da batun tura wata tawagar a karkashin babban wakilin musammun na MDD kan batun zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, mista Robert Serry.

Haka zalika za'a mai da hankali kan sauran batutuwan da suka shafi Libya, Syria, Sudan da Sudan ta Kudu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China