Kwamitin tsaron MDD, ya amince da daukar matakan soji domin murkushe kungiyar 'yan tawayen kasar Rwanda ta FDLR.
A jiya Alhamis din ne dai wakilan kwamitin suka bayyana goyon bayan su ga daukar wannan mataki, na kakkabe mayakan kungiyar daga kasar ta Rwanda, sakamakon kin amincewar da suka yi na ajiye makamansu.
Wata sanarwa daga ofishin shugaban kwamitin ta ce, baya ga kin amincewa da mayakan FDLRn suka yi su ajiye makamai, a daya hannun kuma suna ci gaba da daukar sabbin mayaka.
Sanarwar ta ce, adadin mayakan FDLR kimanin 300 da suka yarda su ajiye makaman su, bai kai yawan da zai nuna da gaske kungiyar ta ke yi ba. Don haka ne ya zama wajibi dakarun gwamnatin jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da na tawagar MDDr su dauki karin matakan kwance damarar 'ya'yan kungiyar.
Ana dai danganta kungiyar ta FDLR da ragowar mayakan kabilar Hutu, wadanda suka aikata laifukan yaki a gabashin janhuriyar dimokaradiyyar Congo, yayin da wasun su ke cikin wadanda suka aikata kisan kiyashin kasar Rwanda cikin shekarar 1994.
Kungiyar raya kudancin Afirka ta SADC, da taron kasashen manyan tafkunan Afirka na ICGLR, sun baiwa kungiyar ta FDLR zuwa ranar 2 ga watan Janairun nan, domin ta cika alkawarin warware damarar yaki, ko kuma ta fuskanci matakan soji. (Saminu)