Kwamitin tsaro na MDD a ranar Talatan nan ta bukaci da a yi saurin wargaza kungiyar 'yan tawaye ta kasar Rwanda dake gudanar da ayyukanta a jamhuriyar demokradiyar Kongo DRC, domin samar da zaman lafiya a kasar da ma shiyyar dake yankin babban tafki.
A cikin wata sanarwa da aka fitar, kwamitin mai mambobi 15 ta nuna takaicinta na ganin har yanzu ba a cimma wannan nufi ba na wargaza kungiyar ta FDLR wadda ita ce na farko a kan jadawalin shirin kawo zaman lafiya a jamhuriyar demokradiyar Kongon da aka sanar a farkon wannan shekarar cewa, za su ajiye makamansu, har ma wassu suka fara yin hakan a watan Mayu.
Mambobin kwamitin sun jaddada goyon bayansu na ganin an yi saurin wargaza wannan kungiya a matsayi na farko a jadawalin kawo zaman lafiya a yankin, tare da nuna damuwarsu game da barazana a cikin gida da ta waje da kungiyar ke haifarwa, da suka hada da rahotanin kwanan nan da ya nuna yadda 'yan kungiyar ke cin zarafin dan adam, da kuma ci gaba da diban mutane, tare da horas da su suna saka su cikin sojojinsu wadanda suka hada da yara kanana, abin da ya sa kwamitin ya jadadda bukatar ganin an wargaza kungiyar domin kawo karshe ga barazanar da take haifarwa.
A cikin sanarwa, har ila yau, kwamitin tsaron MDD ya kuma kara ba da kwarin gwiwwa ga gwamnatin jamhuriyar demokradiya ta Kongo da ta hada kai da rundunar wanzar da zaman lafiya ta majalissar wato MONUSCO domin samun karfin kai harin soji a kan shugabannin kungiyar 'yan tawayen da mambobinsu wadanda manufofinsu ba na demokradiya ba ne illa ci gaba da take hakkin dan Adam. (Fatimah)