in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na kokawa game da karuwar fataucin bakin haure a duniya
2014-10-07 16:08:14 cri
Babban jami'in ofishin yaki da miyagun kwayoyi da manyan lafuffuka na MDD (UNODC) ya bayyana cewa, ana samun karuwar fataucin bakin haure a duniya.

Mr. Yury Fedotov ya shaidawa taron manema labarai cewa, alkaluman bakin hauren da a kan yi fataucinsu daga gabashi, arewaci, da kuma yammacin Afirka zuwa kasashen Turai, sannan daga kudancin Amurka zuwa arewacin Amurka yana karuwa.

Ya ce, wannan sana'a ta fataucin bakin haure zuwa wadannan yankunan na duniya, tana samar da dala biliyan 7, amma akwai yiyuwar alkaluman su dara haka.

Jami'in ya ce, koda yake ofishin na UNODC ba shi da cikakkun bayanai daga mambobin kasashe, sannan ofishinsa bai bayar da nasa cikakkun alkaluman game da bakin hauren da aka yi fataucinsu a sassan daban daban na duniya ba.

Don haka ya yi kira ga mambobin kasashe da su baiwa hukumar tasa goyon baya ta fuskantar musayar bayanai da hadin gwiwa a kokarin da ake na hana fataucin bakin hauren. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China