in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burkina Faso ta kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya
2014-11-24 12:18:38 cri

Hukumomin Burkina Faso sun yi shelar cewar, an kafa wata sabuwar gwamnatin rikon kwarya, a karkashin jagorancin Michel Kafando, da zimmar ya jagorancin kasar nan da zuwa watan Nawumbar badi, lokacin da kasar ta tsai da domin gudanar da zaben shugaban kasa.

Kasar ta Burkina Faso ta shiga cikin halin rikicin siyasa tun bayan da tsohon shuaban kasar Blaise Compaore, wanda ya yi mulkin kasar tsawon shekaru 27 ya tsere daga kasar zuwa Ivory Coast, a sakamakon zanga-zangar jama'a na adawa da kokarin da ya yi na kara wa'adin tsawon mulkin shi.

A karkashin tsarin sabuwar dokar gwamnatin kasar, shugaban kasar Kafando zai jagoranci ma'aikatar hulda da kasashen waje ta Burkina Faso a matsayin shugabanta. Shi kuma tsohon firaministan kasar kanal Isaac Zida a yanzu shi ne ministan tsaro.

Bayan da Compaore ya gudu ya bar kasar, sojojin Burkina Faso sun nada Isaac Zida a matsayin shugaban rikon kwarya, to amma a sakamakon matsin lamba daga kasashen waje, sai shi Zida ya amince ya sauka ya baiwa farar hula mulki karkashin shugabancin Michel Kafando. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China