in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasashen waje dake shirin halartar bikin fareti suna ziyara a birnin Beijing
2015-08-26 11:10:48 cri

Sojojin kasashen waje dake shirin halartar bikin faretin tunawa da cika shekaru 70 da kawo karshen yakin kin harin mayakan Japan suna yawon shakatawa a birnin Beijing, kuma sun yi musayar ra'ayi tare da sojojin kasar Sin.

A ranar Litinin din wannan mako ne, sojojin kasashen waje kimanin dubu daya suka kai ziyara dakin tunawa da yakin kin harin mayakan Japan na kasar Sin da kuma gadar Lugouqiao dake kan kogin Yongding. Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa, sun kara fahimtar tarihin yakin kin harin mayakan Japan da jama'ar Sin suka shirya na tsawon kusan shekaru 14, da kuma babbar gundummawar da jama'ar Sin suka bayar wajen yaki da masu ra'ayin nuna karfi a duniya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China