A taron manema labaran da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar game da bikin faretin, Qu Rui ya yi bayani game da tawagogin soja da na wakilai da 'yan kallo daga kasashen waje da za su zo kasar Sin don halartar bikin.
Qu Rui ya kara da cewa, kasashen waje sun tura tawagogin soja ko wakilai ko 'yan kallo zuwa kasar Sin don halartar bikin faretin tunawa da nasarar yaki da masu ra'ayin nuna karfi a duniya, da neman shimfida zaman lafiya mai dorewa a duniya, da kuma gwada hadin gwiwa mai inganci dake tsakaninsu da sojojin kasar Sin. (Zainab)