in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe 49 za su halarci bikin da kasar Sin za da shirya a ranar 3 ga watan Satumba
2015-08-25 14:04:29 cri

Gwamnatin kasar Sin ta ba da labari cewa, ya zuwa yanzu, kasashe 49 sun tabbatar da halartar bikin tunawa da karshen harin Japanawa da kasar za ta shirya a ranar 3 ga watan Satumba, bikin da ake sa ran shugabanni 30 da manyan jami'ai 19 na gwamnatocin kasashe da kuma shugabanni kungiyoyin kasa da kasa 10 za su halarta.

Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira taron manema labaru a karo na 6 a yau dangane da babban taron cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kin harin mayakan Japan, inda mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Zhang Ming da sauran jami'ai suka halarci taron tare kuma da amsa tambayoyin manema labarai.

Mr. Zhang Ming ya ce, Sinawa na dora muhimmanci sosai kan zumunci da gudummawa da abokai kasashen waje suka baiwa kasar Sin yau da shekaru 70 da suka gabata a yayin yakin kin harin mayakan Japan, kuma Sinawa ba za su taba mantawa da su ba.

An kuma ba da labari cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai karrama lambobin tsoffin sojojin da suka fafata a lokacin yakin kin harin mayakan Japan da lambobin yabo.

Mataimakin ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin Guo Weimin ya shaidawa taron manema labarai a yau cewa, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasar da kuma kwamitin tsakiya na rundunar sojan kasar Sin ne za su ba da lambobin yabo ga tsoffin sojojin da suka fafata a yakin kin harin Japan da kuma iyalansu da tsakatr ranar 2 ga watan Satumba.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China