Majalissar zartaswar tarayyar Najeriya ta rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi 3 na MDD, wadanda suka shafi cinikayyar makamai, da garkuwa da mutane, da kuma batun ayyukan ta'addanci.
Ministan watsa labarun kasar Labaran Maku ne ya bayyana hakan a birnin tarayyar kasar Abuja, bayan kammalar zaman majalissar na ranar Laraba 21 ga wata. Maku ya ce, sanya hannu kan wadannan yarjejeniyoyi uku, ya nuna a fili irin burin Najeriya, na ba da gudummawarta ga ci gaban zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.
Baya ga wadannan yarjejenoyoyi uku, a cewar Maku, ministan shari'ar kasar Mohammed Adoke, ya gabatarwa majalissar zartaswar karin wasu kudirorin MDDr, dake kunshe da tanajin wasu dokoki domin amincewa.
Ministan watsa labaran ya kara da cewa, sanya hannu kan yarjejeniyar cinikayyar makamai, zai ba da damar dakile sarrafar makamai masu hadari ba bisa doka ba. (Saminu)